A ranar Lahadi ne aka ci gaba da kai farmaki kan sarakunan gargajiya a yankin Kudu maso Gabas tare da yin garkuwa da wasu sarakuna biyu a jihar Imo.
Bayan sun tafi da sarakunan, ‘yan bindigar sun kuma kona gidajensu da ababen hawa.
Sarakunan gargajiyan da abin ya shafa sun hada da Acho Ndukwe na Amagu Ihube da Paul Ogbu na Ihitte Ihube, dukkansu a karamar hukumar Okigwe ta jihar.
‘Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da shugaban matasan Ulolo Okigwe wanda ba a bayyana sunansa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Majiyoyin al’umma sun shaida wa wakilinmu cewa, an kai farmakin ne tun daga karfe 12 na dare har zuwa karfe 1 na safiyar ranar Lahadi.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce, “ A cikin motocin Hilux ne suka zo suka yi garkuwa da sarakunan biyu tare da kona gidajensu da ababen hawa.
“Sun kuma yi garkuwa da shugaban matasan Umuololo-Okigwe. Eze Ndukwe shine shugaban majalisar sarakunan gargajiya a karamar hukumar Okigwe.
“Har ila yau, shi ne shugaba kuma shugaban otal na Genesis, dake garin Okigwe. Babu wanda zai iya fahimtar wannan harin. Al’ummomin sun ruɗe”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mike Abattam, ya bayyana cewa rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
Ana samun karuwar hare-haren da ake kaiwa cibiyar gargajiya a yankin Kudu maso Gabas a ‘yan kwanakin nan.
Idan za’a iya tuna wa, An yi garkuwa da basaraken gargajiya na tsohuwar masarautar Atta da ke karamar hukumar Njaba Edwin Azike a ranar Alhamis kuma aka kashe shi a ranar Juma’a tare da jefar da gawarsa a dandalin kasuwa.
Kana an Kuma yi garkuwa da basaraken gargajiya na tsohuwar masarautar Mbutu, Damian Nwaigwe a ranar Alhamis kuma aka sake shi a ranar Asabar.
Har ila yau, an yi garkuwa da basaraken gargajiya na Achi Mbieri, Henry Madumere, a ranar 19 ga watan Nuwamba, a hanyar zuwa taron a Iho a karamar hukumar Ikeduru.
A ranar 19 ga Oktoba, wasu ‘yan bindiga sun kai hari hedikwatar karamar hukumar Njaba da ke Nnenasa inda suka harbe sarakunan gargajiya da ke taron masu ruwa da tsaki.
Yayin da wasu masu rike da sarautun gargajiya biyu suka samu raunuka a harbin bindiga kuma an garzaya da su asibiti, wasu biyu kuma sun mutu nan take.
Comments 1