Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton yan kungiyar Inyamurai ta IPOB ne sun farmaki ofishin yan sanda tare da kona ta kurmus gami da hallaka jami’ai biyu a Jihar Abia.
Da sanyin safiyar yau ne yan bindigar suka farmaki ofishin yan sandar na Upumiri Ubakala dake Karamar Hukumar Umuahia ta Kudu.
Wani jami’in dan sanda ya shaida cewa gabannin faruwar al’amarin, sai da suka samu bayanan sirri kan cewa za a kai harin, don haka a rufe Ofishin ko kuma a jibge jami’an tsaro, amma aka yi kunnen uwar shegu.
Wannan hari shine na baya-bayan nan da aka kai a shiyar Kudu maso gabashin kasar nan, duk da cewa a baya an kai makamancinsa a Jihar Enugu.
Yanzu haka hare-hare na kara yawaita a shiyar, inda aka kona ofishin yan sanda ta Bende kurmus, kuma ya faru ne kwanaki bayan da wani harin makamancin wannan a Uzuakoli dukkanin su a jihar Abia.