A ƙalla mutane sama da arba’in ne suka kwanta dama sakamakon wani mummunan farmaki da yan fashin daji suka kai kasar Feru dake karamar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.
Kauyukan da yan fashin dajin suka yi ɓarna sun hada da Tsauni da Gudan-Baushi da Gidan-Adamu da Wari gami da Gudan-Maidawa.
Wani mazaunin wannan yanki mai suna Mallam Buba Faru, ya tabbatar da cewa yan fashin dajin sun fantsamo ne kan babura sama da 100 inda suka afka wa ƙauyuka da ba su da tazara da garin Faru.
Buba Faru ya kara da cewa maharan sun yi ta harbin kan mai uwa da yayin da kuma suka kona gidaje gami da rumbun adana hatsi na al’ummar da abin ya shafa.
“Kawo yanzu dai an gano gawarwaki sama da arba’in, wanda yan sa kai suka zakulo”
“Kuma Inshallah a ranar Juma’a ne za’a bisne wadannan gawarwaki bisa tanadi irin na addinin Islama” cewar Buba.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar ta Zamfara Muhammad Shehu ya tabbatar da aukuwar lamarin, to sai dai ya ce mutane 35 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin.