By Abbas Yakubu Yaura
Rikici ya barke a ranar Alhamis yayin da wasu ‘yan fashi suka kai hari a unguwar Idi-Ape da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
A cewar rahoton, ‘yan sanda biyu sun mutu tare da ‘yan fashin yayin harbe-harbe a lokacin da suke gudanar da aikin su.
Ba a iya tabbatar da ko ‘yan bindigar sun yi nasarar sace motar kai kudi bankin ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa motar dakon kudin ta fito ne daga daya daga cikin sabbin bankunan zamani da ke kusa da filin gwajin.
Sai dai kuma duk kokarin tabbatar da faruwar lamarin daga wajen ‘yan sanda ya ci tura.
Kiraye-kirayen da aka yi wa mai magana da yawun ’yan sandan jihar Oyo bai samu na saraba ga manema labarai.