Hukumar ‘yan sandan jihar Neja, sun yi nasarar ‘yanto mutum daya cikin hudu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar. Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da hakan a garin Minna a yau Lahadi.
ASP Wasiu ya ce ‘yan sandan a ranar 25 ga watan Disamba, sun samu bayanai da ke nuna cewa ‘yan bindiga sun kai hari a garin Unguwan Gambo dake karamar hukumar Rafi inda suka yi garkuwa da mutum hudu. Sai dai ya ce; sun yi nasarar ‘yanto mutum daya ba tare da samun matsala ba, a yayin da suke ci gaba da aiki tukuru wajen ‘yanto sauran da cafko ‘yan bindigar.