An kama wani da ake nema ruwa a jallo a jihar Osun, Rasheed Hammed, wanda aka fi sani da Oko-Ilu.
Oko-Ilu, wanda ke ta’addanci a yankin Ede, kuma ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, jami’an hukumar yaki da kungiyar asiri ta rundunar ‘yan sandan jihar sun kama shi.
An kama shi ne da misalin karfe 4 na safe a maboyarsa da ke babban birnin jihar kuma a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda.
Jami’an tsaro na zawarcin Rasheed, mai sana’a walda, bisa zarginsa da kashe mutane da dama a yankin Ede.
Nishadi: Don Kana Kashe Kudade A Kaina Baka Da Tabbacin Samun Soyayyata – Jaruma Sandra Ifudu
Ana zargin ‘Rasidi Baale Oko’lu’ da mutuwar Hassan Adedeji, wanda ya kammala babban Diploma a bangaren sha’anin kudi da sha’anin banki a kwalejin Federal Polytechnic, Ede, yana jiran takardar kiransa da aka yi masa, da kuma wani direban Okada,
Don haka rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta bayyana cewa, duk wanda ya boye shi za a dauke shi a matsayin mai laifi.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya fitar a watan Maris, ya ce ana neman Rasidi ne bisa laifukan kisan kai, kone-kone, kisa na dake da alaka da asiri da kuma fashi da makami.
Ya ci gaba da cewa, “Wadan ake zargin ya na haddasa fitina a Ede da jihar Osun baki daya.