Akalla ‘yan takarar gwamna 17 na jam’iyyar PDP sun yi wata ganawar sirri da gwamnan Rivers, Nyesom Wike, kamar yadda The Nation ta rawaito.
An tattaro cewa ‘yan takarar daga jihohin Sokoto, Jigawa, Kaduna, Katsina da wasu 13 sun kai wa Wike ziyara a gidan sa dake Rumueprikon a karamar hukumar Obio-Akpor.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Zulum Ya Ziyarci Garin Bama, Wanda Ya Kasance Tungar ‘Yan Boko Haram
Rahotanni sun ce ‘yan takarar sun isa Fatakwal ne da misalin karfe 8 na dare sakamakon rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar gabanin zaben 2023.
An ce sun je rokon Gwamnan ya yafewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu da sauran shugabannin PDP da suka bata masa rai.
An tattaro cewa taron yana ci gaba da gudana har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoton.
Ba a iya sanin ko jam’iyyar Atiku ce ta tura su ba ko kuma sun je ne da son ransu.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an fara taron ne da misalin karfe 8:30 na dare.
A wani labarin kuma, An Kama Mutane 30 Da Ake Zargi Da Hannu A Wani Rikicin ‘Yan Kungiyar Asiri
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue a ranar Talata ta tabbatar da kama wasu mutane 30 da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kungiyar asiri a garin Gboko da ke karamar hukumar Gboko a jihar Benue.
Daily Trust ta tattaro cewa mutane uku ne ake zargin an kashe a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kungiyar asiri da ya faru a karshen mako.