Dubban ‘yan kasar Gambia ne suka fito kan tituna domin nuna adawa da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 4 ga watan Disamba.
Zaben wanda ‘yan takara shida suka fafata, shugaban kasar mai ci Adama Barrow ne ya lashe zaben.
Mista Barrow wanda ya fafata a zaben a karkashin tutar jam’iyyar NPP, ya samu kuri’u 457, 519 inda ya doke abokin hamayyarsa Ousainou Darboe na jam’iyyar United Democratic Party (UDP) da ya Samu kuri’u 238,253.
Jim kadan gabanin sanarwar da zaben, da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta fitar, Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘yan takarar jam’iyyar adawa uku sun ki amincewa da sakamakon zaben.
Yan takarar sune; Ousainou Darboe na jam’iyyar United Democratic Party (UDP), Mama Kandeh ta Gambia Democratic Congress (GDC), da Essa Faal, ‘yar takara mai zaman kanta, duk sun yi watsi da sakamakon kuma sun janye wakilan jam’iyyarsu inda suka ki sanya hannu.
A yau Litinin, dimbin magoya bayan Mista Darboe sun kewaye titin Kairaba Avenue inda yake zaune.
Yayin da wasu suka yi tattaki don murnar nasarar da Mista Barrow ya samu, wasu kuma suna son ‘adalci’. Inda suke ta rera ‘aye ji’, wanda a zahiri fassararan shi ke nuna cewa ayi Adalci’ a cikin yaren Mandinka.
“Ina son adalci, ina so a cire Barrow daga fadar gwamnati a yanzu,” in ji Jami Amfal, daya daga cikin magoya bayan.
Sauran magoya bayan sun yi magana da Jaridar PREMIUM TIMES a irin wannan magana.
“Ousainou Darboe ne ya lashe zaben. Muna son Barrow ya sauka, muna son a sake zaben,” in ji wani mai goyon bayan da ya harzuka.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa an baza ‘yan sandan Gambia da dama kan titi domin dakile tabarbarewar doka da oda.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, karin magoya bayansa na ci gaba da tururuwa akan tituna.