• Dan fafutukan kafa kasar Yarbawa Sunday Igboho, ya shiga hannu a Cotonou.
• Jami’an tsaron farin kaya ne suka kama Sunday Igboho.
• Yau ake saran zai iso Nigeria daga Jamhoriyar Benin.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, An kama mai fafutukar kafa kasar Yarbawa Sunday Adeyamo, Wanda akafi sani da Sunday Igboho a garin Cotonou dake Kasar jamhoriyar Benin.
An kama shi ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Cotonou, a daren jiya Litinin, kamar yadda wani na kusa da lamarin ya shaida wa wakilin mu.
Rundunar tsaro ta farin kaya dake jamhoriyar Benin ce, ta kama Igboho makon ni uku bayan Rundunar DSS ta Nigeria, ta bayyana shi a matsayin wanda take neman ruwa a jallo, da laifin tara makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma cin amanar kasa, wanda ya sha karyata wadannan zarge-zarge.
Majiyar mu ta labarto mana cewa, za’a dawo Igboho gida Nigeria a yau Talata daga Kasar Jamhoriyar Benin l, daya daga cikin magwafciyar kasar dake yammacin nahiyar Africa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babar Sallah: Shugaban Majalissar Dokokin Kaduna ya bukaci Musulmai da su rungumi sadaka
” Rundunar tsaron farin kaya ta Jamhoriyar Benin ce ta kamashi a Cotonou, lokacin da ya ke yunkurin tserewa zuwa kasar Jamus a daren ranar Litinin, Inda jami’an na Benin, za su mika wa takwarorin su na Nigeria shi, a yau Talata.” Inji shi
Idan za’a iya tunawa dai, jami’an yan sandan farin kaya sun farmaki wani matsugudin Igboho a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2021 dake Ibadan, inda suka kama mabiyan shi goma sha biyu, biyu kuma suka mutu a wani musayan wuta da su ka yi.
Gwamnatin tarayyar Nigeria dai tuni ta ankarar da hukumar kula da shige da fice, da Hukuma Hana fasa kwabri ta kasar, kan kokarin dakatar da Sunday Igboho tserewa daga Nigeria.
Sai dai Koda aka tuntubi wani Mamba a tawagar Igboho, Pelumi Olajengbesi ya ce zai yi magana dazaran ya tuntuni Lauyan su Yomi Aliyu SAN an jima.
Kazalika a kokarin da akayi na tabbatar da kamun wanda ake zargin, an tuntunmi Mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS, Peter Afunanya, ta sakon kartakkwana, amma haryazu wa hada wannan labarin bai ce komai ba.
Ku gamashi mu a fulance namiji bai gudu said dai ya mutu, sannan wanda yake Benin da wanda yake Nigeria basu da bambamci ga Buhari in yana son kamasu.