Akalla malamai 233 dake da takardar shedar bogi gwamnatin jihar Kaduna za ta kora daga bakin aiki, in ji shugaban hukumar ilimin na bai daya ta jihar Tijjani Abdullahi.
Shugaban wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kaduna, babban birnin jihar a ranar Alhamis, ya kuma jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen gudanar da jarabawar cancantar malaman makarantun gwamnati a jihar.
Abdullahi ya kara da cewa, a kokarin hukumar na ganin malamai sun gudanar da aikin tantancewar an tsara fara tantancewar ne Nan da watan watan Afrilu Mai zuwa.
A cewarsa, manufar ita ce a tabbatar da cewa dukkan malaman sun samu takardun shaidar da ake bukata wanda ya kunshi muhimman abubuwan da suka dace na aikin koyarwa.
Ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, hukumar ta tantance takardun shaida Malamai guda 451 daga cibiyoyi 13, inda ya kara da cewa daga cikin alkaluman an gano takardun shaidar karatun Malamai guda 233 ‘na bogi ne.
Abdullahi yace malamai 233 dake da takardar shedar bogi za a sallame su daga jerin ma’aikatan jihar tare da fuskantar cikakken hukuncin doka.
Ya kara da cewa, a wani bangare na bayyana gaskiyan hukumar, za a sanya sunayen malamai 233 masu takardar shedar karya a shafin gwamnatin jihar.
Shugaban SUBEB yace, “Hukumar ilimin na bai daya ta Jihar Kaduna (KADSUBEB) tana son sanar daku abubuwan dake faruwa a baya-bayan nan a kokarinta na inganta matakan ilimi a makarantun gwamnati.
Kazalika “Izuwa yanzu, hukumar ta tantance takardun shaida 451 ta hanyar tuntubar hukumomin da suka bayar da takardar shaidar. Tara daga cikin cibiyoyi 13 da aka tuntuba sun amsa, ya zuwa yau.
‘”Hukumar ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da Cibiyar Malamai ta kasa, Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya, da Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Zariya domin gudanar da atisayen.”