Labarin yadda wata ƴar aiki ta taimaki rayuwar iyayen ta ya sanya mutane da dama sun ƙara ɗaukar himma.
Budurwar ta bayyana yadda ta taso cikin wahala aka haife ta cikin gidan ƙasa ta yadda ta bar gida bayan ta kammala karatun firamare. Rahoton Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya kaddamar da cibiyar yaƙi da ta’addanci
Ta bar gida ta koma cikin birni inda take aiki a matsayin ƴar aiki a gidaje da dama tana tara ƴan kuɗaɗen ta.
Budurwar ta bayyana cewa ta daɗe tana da burin ginawa iyayen ta gida. Bayan ta kwana biyu a birni, ta dawo gida inda ta sauya fasalin gidan ƙasar da iyayen ta suke a ciki.
Ta kuma siyo sababbin kujeru, teburi da kuma gado waɗanda za ayi amfani da su a gidan. Matashiyar budurwar tace tan fatan watarana ta siyawa iyayen ta motar hawa.
A shafin ta na TikTok, ta sanya wani bidiyo inda ta nuna gidan ƙasar da kuma kayayyakin da ta kawo.
Ku kalli bidiyon a nan