Wata Kotu a kasar Brazil ta umarci shugaban kasar Jair Bolsonaro da ya biya wata Yar JArida diyya bisa kazafi da ya yi mata
Mista Bolsonaro ya yi ikirarin cewa yar Jaridar ta bukaci bada kanta ga wani da zai bata bayanai kan shugaban kasar a shekarar da ta gabata, to sai dai alkalin kotun ya ce kalaman na Bolsonaro ya bata wa yar jaridar suna ne.
Bisa ga haka yanzu kotun ta umarce shi da ya biya ta diyyar dala dubu biyu da dari biyar, amma kuma idan hukuncin bai yi mishi ba yana iya dauaka kara.
Yar Jaridar mai suna Mis Campos Mello wacce ta lashe kyautar gwarzuwar yar Jaridar ta Jaridar Folha de S. Paulo, ta wallafa a shafin ta na Tuwita cewa wannan hukunci da kotu ta yanke nasara ce ba ga ita kadai ba sai dai ga dukkanin matan duniya.
Kazalika Kungiyar Yan Jarida mai fafutukar kawar da cin zarafin mata ta ce lallai wannan babbar nasara ce ga aikin nasu.
Mista Bolsonaro wanda ya dare karagar mulki a shekarar 2019 ya yi bakin jini gurin yan jarida ta fuskar soke lamirin shi na shugabanci.