By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mata 300 ne daga kananan hukumomin Dukku da Nafada a ranar Lahadin da ta gabata ne suka ci gajiyar shirin bada tallafin naira 10,000 da ‘yar majalisar wakilai Aishatu Dukku ta gabatar a matsayin tallafi.
Dukku ta ce shirin karfafawa mata an yi shi ne domin inganta sana’o’in gida na mata a yankin, inda ta kara da cewa a nan za a ci gaba da kasancewa a mataki na biyu.
A cewarta, tabarbarewar tattalin arziki da ya durkusar da duniya ya jefa iyalai da dama cikin talauci, inda ta jaddada hakan a matsayin dalilin raba kayayyakin.
‘Yar majalisar ta yabawa gwamnan jihar, Muhammadu Yahaya, da uwargidansa, Hajiya Asma’u, wadanda suka halarci bikin, na samar da yanayi mai kyau ga mata a jihar, wajen bayar da gudunmawa mai ma’ana ga harkokin mulkin jihar.
Dukku ta ce, “Gwamnatin Inuwa tana aiwatar da ayyuka da dama a mazabar musamman wadanda ke da nufin daukaka darajar ilimin ‘ya’ya mata.
A nasa bangaren, Gwamna Yahaya, ya ba da tabbacin kokarin gwamnatinsa na ba da fifiko ga ilimin ‘ya’ya mata a kananan hukumomin Dukku da Nafada, musamman wajen aiwatar da wasu ayyuka tare da samar da ruwa.
Yahaya wanda ya yi alkawarin yashe dukkan madatsun ruwa na karamar hukumar Dukku saboda kalubalen da suke fuskanta na tsawon shekaru na ruwan sha, ya kuma kaddamar da aikin gyaran rijiyoyin burtsatse daga kogin Gombe Abba zuwa cikin garin Dukku.
Yayin da yake yaba wa ‘yar majalisar kan shirin karfafawa, Gwamna Yahaya ya yi alkawarin ci gaba da hada kai da ita wajen inganta rayuwar al’ummar mazabar.
Ita ma uwargidan gwamnan, Asma’u Yahaya, tace ba da gudummawar za ta taimaka sosai wajen rage matsalolin da mata ke fuskanta a gida duba da matsayinsu na ’yan gida da kuma masu gina kasa.
Sannan ta kuma gargadi matan da su guji yin amfani da kudaden da aka ba su ta hanyar da bata dace ba.
Comments 1