Wata yarinya ‘yar shekara 13 mai suna Zuwaira Ahmed da ke kauyen Kagara da ke karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ta haddace tare da rubuta cikakken Alkur’ani Mai Girma Izufi 60.
Da yake jawabi a wajen bikin karrama yarinyar a ranar Asabar, Hakimin Mahuta, Alhaji Bello Abdulkadir, ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba.
Ya bayyana cewa wannan babbar nasara ce ga al’umma, da ma jihar baki daya, musamman a bangaren ilimin addinin Musulunci.
KARANTA ANAN: Murabus Ɗin Iyorchia Ayu Babbar Annoba Ce Ga Jam’iyyar PDP – Aniagwu
Abdulkadir yabawa iyaye a yankin, malamai da sauran shugabannin al’umma kan yadda suke kula da tarbiyyar ‘ya’yansu yadda ya kamata, yana mai kira gare su da su ci gaba da dagewa.
Danejin Katsina ya baiwa sarakunan jihar tabbacin cigaba da bada goyon baya ga duk wani abu da ya shafi addinin musulunci domin cigaban yankin baki daya.
Shugaban karamar hukumar Kafur, Alhaji Garba Abdullahi-Kanya ya yaba da kwazon yarinyar tare da bada tabbacin tallafawa karatun ta a matakin Sakandare har zuwa makarantar gaba da sikandire.
Shugaban makarantar ta Madrasatul Tahfiz, Sheikh Sani Kagara, ya ce an kafa makarantar ne da nufin samar da ingantaccen ilimin addinin Musulunci a tsakanin matasa a cikin al’umma.
A wani labarin kuma: Wasu Daga Cikin Abubuwan da Zasu Faru Bayan Mutuwar Sarauniya Elizabeth II
A makon nan da muke shirin bankwana da shine sarauniyar Burtaniya Elizabeth II ta mutu, wanda mutuwarta zai haifar da sauye sauye da dama a kasar.
Kudin ƙasar zai fuskanci sauyi ta yadda yake a yanzu da kuma zuwa lokacin da mulkin Sarki Charles III zai kan kama.
Yanzu haka dai hoton Elizabeth ne a jikin kudin, kuma sannu a hankali za a fara buga sabbin kudi wadanda zasu fito da Sarki Charles III maimakon na mahaifiyarsa.