Mahukunta a Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya sun yi kira ga gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta daukan matakin kawar da matsanancin da yara kanana ke fama da cewa idan ba ayi taka-tsantsan ba za a ita rasa yara akalla 34,000 a jihar.
Premium Times sun labarto cewa; jami’in asusun dake kula da shiyyar Bauchi Bhanu Pathak ya bayyana haka wa gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku a garin Jalingo ranar Alhamis.
“Bincike ya nuna cewa yara 34,419 a jihar Taraba na fama da matsanacin yunwa da idan ba a maida hankali na za a iya rasa su.
Pathak ya kuma ce akwai yara kanana sama da 75,000 da ba a yi musu allurar rigakafin cutar shan inna da sauran cututtukan dake kisan yara ba a jihar.
Sannan har yanzu akwai yara sama da 500,000 da basu zuwa makaranta a jihar.
“Hakan ya kara daburta matsalolin ‘yan gudun hijira da jihar ke fama da shi. Sannan muna
kira ga gwamnati da ta zage damtse wajen ganin an kawar da wadannan matsaloli.
A nashi jawabin gwamnan jihar Darius Ishaku ya yabawa tallafin da UNICEF ke ba jihar musamman a bangarorin kiwon lafiya, ilimi, tsaftace muhalli da sauran su.
Ishaku ya kara da cewa gwamnatin jihar ta taka rawan gani a fannonin kiwon lafiya da kula da yara.
“Sai dai kuma matsalolin dake bullowa daga sansanonin ‘yan gudun hijira ya fara fin karfin gwamnati da dole sai an rika tallafa mata.
“Ina tabbatar mu da cewa gwamnati baza ta yi sakwa-sakwa ba ki kuma ja da baya ba wajen sauke duk nauyin mutanen da dake kanta ba.