A jiya juma, yara uku sun tsallake rijiya da baya, bayan da wani bene Mai hawa uku, ya fadi kan ginin gidan su a jihar Egunu.
Benan dai ya fadi ne a dakin shakatawa na wani gida, dake kusa da shi, ya yin da Yara uku ke cikin dakin suna karatu.
Amma yanayin karar da ginin ya fara yi ne tun kafin fadu war shi, ya sa yaran suka gudu zuwa dakin kwanan inda mahaifiyarsu ke kwance.
Mataimakin Shugaban karamar hukumar Aninri na jihar Enugu, da kuma Mahaifin yaran Mr Ndukwe Okechukwu Bamidele, sun tabbatar wa da manema labarai afkuwan lamarin., Inda suka bayyana cewa, yaran sun tsira bayan da suka gudu wajan mahaifiyar su. kafin faduwar ginin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ta sanadiyar Fim na iya Hausa, inji Amina Amal
Bamidele ya bayyana cewa, yadda yaran suka tsira ya nuna cewa, wannan taimakone daga Ubangiji.
Kazalika da aka tuntumi jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Enugu, Mr Daniel Ndukwe, ya tabbatar da afku war lamarin, inda ya bayyana cewa, rundunar tasami labarin faruwar lamarin da musalin karfe 7 na dare.
Ya kuma kara da cewa, tuni jami’an yan sanda suka Isa inda lamarin yafaru ,domin killace wurin.
“Kuma karamin binciken da muka gudanar ya nuna cewa, Babu wanda ya rasa ransa sanadiyar lamarin, Amma dazarar mun sami wani bayani, zamu sanar da al’uma” inji shi.
Comments 1