Yariman Birtaniya mai jiran gado Harry da kuma budurwarsa Meghan sun sanar da samun karuwar ƴa mace a ranar Juma’a kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
Sai dai labarin samun karuwar ya buwayi duniya ne a yau Lahadi bayan da Kakakin Yariman ya sanar da wannan abin farin ciki.
Kuma tuni aka rada mata suna da Lilibet “Lili” Diana, a sanyin safiyar yau ɗin.
Wannan suna dai na Lilibet suna ne na sarauta dake zama inkiyar sunan Sarauniyar Ingila, yayin Lili kuma ke Kasancewa sunan kakanta ta wurin uwa.
A yanzu haka Lilibet ita ce ta takwas a jerin ƴaƴan gidan sarautar Burtaniya.
Har kawo yanzu dai ba a bayyana hoton jaririyar ba, yain da muke kawo muku wannan rahoto.
Yanzu haka wannan karuwa ta zamo ta biyu kenan a wurin Harry and Meghan.