Yarima Zazzau, Alhaji Munir Ja’afar ya aurar da ‘ya’yansa mata biyu. A ranar Asabar din 26 ga watan Disambar 2020 ne ya aurar da ‘ya’yansa mata Hafsat da Fatima, inda aka daura auren a garin Zariya.
Hafiz ne ya auri Fatima a yayin da kuma Mahmood ya auri Hafsat.
Daga cikin wadanda suka samu halartar daurin auren sun hada da Daraktan NIMASA, Bashir Jamoh, Kwamishinan kudi na jihar Kaduna, Bashir Saidu, Babban Joji, Mukhtar Dodo, tsohon dan majalisar Tarayya, Sani Sha’aban da kuma Yusuf Datti Ahmed.