Shafin gwamnatin jihar Legas ta wallafa waɗansu hotuna inda ta yi nuni da cewa; wannan yarinya ta zama gwamnan jihar Legas ne na yini daya a ranar juma’a 26 ga watan Maris din 2021.
Gwamnan jihar Sanwo-Olu ya ba wannan yarinya mai suna Eniola Ajala wannan damar ne sakamakon lashe gasar Spelling Bee competition ta shekarar 2018/2019.