Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari yace yarjejeniyar da gwamnatinsa tayi da ‘yan bindiga ta dauki tsawon watanni bakwai ne kawai.
Gwamnan yace a halin da ake yanzu babu sauran wata yarjejeniya tsakanin gwamnatinsa da ‘yan bindigar, saboda sun saba alkawarin da suka dauka.
Masari ya bayyana haka ne a yayin da take tattaunawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-kashe-mutane-13-a-katsina/
Gwamnan ya kulla yarjejeniyar da ‘yan bindigar har sau biyu, na farko a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2017, sai na biyun a ranar 4 ga watan Satumbar shekara ta 2019.
Bayan cimma yarjejeniyar an dan samu kwanciyar hankali a jihar, Amma a ‘yan kwanakin da suka gabata an kashe mutane sama da 200 a kauyukan Faskari, Batsari da sauransu.
Gwamnan yace duk da sharudan da suka bawa gwamnati kuma an cika musu kaso 80 zuwa 90 Aamma sai da suka karya alkawari, dan haka babu wani sauran sassauci da zasu gani.