Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro Mai shekara 5, Mai suna Yusha’u Usman sanadiyar afkawa rijiya da ya yi a garin Zangon Dinya, dake karamar hukumar Bagwai na jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Abdullahi ne ya tabbatar wa da manema labarai mutuwar yaron a jiya juma’a, a garin Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa, lamarin ya afku ne a daran ranar Alhamis din da ta gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin shiga ta harkan fim, Zulaihat Ibrahim Zpretty
” Munsami Kiran waya daga yankin Bichi da musalin Karfe 08:30 na dare, daga Wani mutum Mai suna Muhammad Usman, inda muka tura da jami’an ceto da musalin karfe 08:45 yankin da lamarin ya faru domin Kai dauki” inji shi.
Ya kara da cewa, yanzu haka hukumar tafara gudanar da bincike kan lamarin, domin sanin musabbabin afkuwar lamarin.
Abdullahi ya ci gaba da cewa, Gawar yaron da ya fada a rijiyan, an mika shi ga Shugaban yankin Zangon Dinya na karamar hukumar Bagwai Malam Yahaya Sule, domin jagorantar yin jana’izar shi.
A wani labarin Kuma na daban.
Tsohon Gwamnan Jahar Jigawa Alhaji Sule Lamido yace Nigeria bazata taba rabewa, sabudda Shuwagabannin ta kansu a hade yake wajen cimma muradun su akan talakawa, ba tare da duba bambancin su ba.
Dayake jawabi ga taron Matasa Wanda sukayi kira a gareshi daya tsaya takarar Shugaban Kasa a Shekarar 2023, a lokacin taron bikin murnar zagayowar ranar haihuwar sa a shekaru 73, yace Nigeria batada karfin da zata rabe gida biyu.
Ya tambaya ” wazai raba ta” talaka daga Jigawa ko na Sokoto ko kuma Wanda ke Bayelsa? Shin Mai faci Inyamuri ko kuma macen Yoruba Mai saida Kalanzir a kusa da hanya, ko kuma Dan Okada a Delta?
Basu da karfin hada kansu domin suna fuskantar Talauci. Mun tafi da mutuncin su da tunanin su, domin kada ma su shirya domin neman kasar ta rarrabe.
“Acan sama, mu Shuwagabanni mun hada kanmu. Bazamu taba bari Nigeria ta rarrabe, domin idan ta rarrabe zamu rasa abubuwa da dama, amma talaka babu abunda ya rasa, To mima zai rasa? Dama tuni Yana cikin talauci, babu abunda zai rasa sai talaucin sa.”
Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa, jinin mutane nata kwarara a kasar sabudda rashin iya Shugabanci a Karkashin Gwamnatin APC ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari