Rahotannin da jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, tun da sanyin safiya yau Laraba ce aka rufe hanyar zuwa fadar Sarkin Kano, inda Kotun da ake shari’ar ta ke, jibge da jami’an tsaro.imda hakan ke nuna cewar, da yuwuwar cigaba da shari’ar Sheikh Abduljabbar.
An gurfanar da malamin ne a kotun shari’ar Musulunci da ke Ƙofar Kudu, bisa zargin yin kalaman ɓatanci,ga fiyayyan halitta.
A zaman kotun na ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata, mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya fara sauraron ɓangarorin biyu. Sannan aka ɗage zuwa yau 18 ga watan Agusta shekarar 2021.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Bauchi ya fitar da sunayen kwamishinonin 17
Don haka, ku ci gaba da bibiyar jaridar Dimokuradiyya domin jin yadda shari’ar za ta kasan ce.