A wannan rana ta Litinin wato 21 ga wagan Satumba shahararriyar jarumar nan ta masana’antar Bollywood ta ƙasar Indiya wato Kareena Kapoor ta keyin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta inda aka haifeta a makamanciyar wannan rana.
An haifeta a ranar 21 ga watan Satumba na shekarar 1980 inda ta cika shekaru 40 cif-cif a duniya, an haifeta a Maharashtra dake birnin Bombay na ƙasar Indiya, iyayen da suka haifeta sune Randhir Kapoor da kuma Babita.
Tana cikin iyalan nan da ake kira da Kapoor kuma ƙanwa ce ga shahararriyar jarumar nan wato Karisma Kapoor watta ita Karisma take a matsayin bazawara a halin yanzu tunda sun rabu da mijinta tun a shekarar 2016.
Kareena Kapoor ta fara yin fim tun tana da shekaru 20 a duniya inda ta fara yi tun a shekarar 2000 kuma har yanzu tana yin fim, sannan tayi aure a shekarar 2012 inda ta auri jarumi Saif Ali Khan kuma a iya tsawon shekaru 8 da sukai aure ɗa ɗaya suka haifa.
Jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta tattauna da wata mai bibiyar India sosai kuma masaniya wadda take a jahar Kano wato Ameena Abdurrahman Hassan Birget Gama inda jaridar ta tambayeta kome zata iya tunawa dangane da jaruma Kareena Kapoor duba da cewar yau take murnar zagayowar ranar haihuwarta?
“Eh to jarumar tayi fina-finai da dama masu nishaɗantar wa, amma ni abu guda biyu zan iya tunawa da sukafi birgeni kuma suka bani mamaki.
1. Lokacin da suka yi rigima a wajen shooting ɗin fim maisuna Ajnabee ita da Bipasha Basu wanda suka yi abin da ake cewa Cat fighting sabo da kishi.
2. Sai kuma matsananciyar soyayyar data nunawa Shahid Kapoor inda wata rana har daɗin soyayya yasa ta saka hotonsu da sukayiwa juna sumbata ta musamman suka yi gangancin sakashi a social media inda abin ya yamutsa hazo sosai”
Daga ƙarshe dai Kareena Kapoor ta godewa dukkanin mutanen da suka taya ta murna wato masoyanta inda ta yiwa kowa fatan alkhairi da godiya ta musamman duba da yadda har yanzu ake ƙaunarta sosai da sosai.