• A yau me wadannan jaruman Kannywood suke cika shekara 13 da aure.
• Su ne ma’aurata na farko a Kannywood da su kafi dade wa a tare bayan rabuwar Mansura Isa da Sani Danja.
• A cikin auren na su Allah ya Albarkace su da Yara 3 dukannin su mata
Daga Mukhtar Yakubu Kano.
A wannan rana ta 28 ga watan Yuni za a iya cewa, rana ce ta alfahari ga tsohuwar jaruma Muhibbat Abdussalam tare da maigidan ta, Darakta Hassan Giggs da iyalan su da ma dukkan masoyan su.
Domin kuwa a wannan rana ce suka cika shekaru 13 da aure su, kuma suna zaune har zuwa yanzu, ba tare da sun rabu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ga nduje zai biya wa Yara marasa galihu guda 10,000 Kudin NECO
A cikin wannan shekaru da suka yi na zaman auren, Allah ya yi musu arzikin haihuwar yara guda uku dukannin su mata, wadanda a yanzu ma ‘yar su ta farko mai suna Humaira, ta fara zama Budurwa.
A yanzu dai bayan rabuwar auren Mansurah Isah da Sani Danja, ana gani Muhibbat Abdussalam da Hassan Giggs su ne’ yan fim da suka fi dadewa, suna zaman aure tare. Muna fatan Allah ya kara arziki da zaman Lafiya a tsakanin su.
Comments 1