Jaridar Dimokuradiyya ta yira da Zaharaddeen A Abdallah Marubuci, Mawaki kuma mai sharhi da fashin baki akan al’amurran yau da kullum. Daga masana’antar fina finan Hausa Kannywood., Inda ya jaddada cewa, yananan akan bakar shi.
Mutane dayawa basusan cewa banida aure ba sabida ina kare mutuncina dana addina iya gwargwadon yanda Allah yabani iko kamar yanda Allah yace: Qur’an Sura 64: V. 12
Ni bamai kudi baneba sannan kuma ban Shahara ba a idanun duniya.
Mutane sunyarda cewa idan bakayi kudiba daga Allah amma idan bakayi aureba laifinka ne.
Toh yau gashi rijiya tabayar guga yahana. Naje neman Aure ance baza abaniba sabida inayin waka.
Hakan yadameni amma raina bai baciba sabida nayarda dakaina, mutuncina dakuma addinina.
Tambaya anan itace: Waka sata ce? Ko Waka Shirka ce? Da inzama Mawaki danayi fashida makami wanne ne laifi? Shin dana zama dan Ta’adda konayi Kidnapping danayi waka wane ne laifi? Miye laifin waka idan har nayita akan matakin shari’a?
Nayi karatu na addini dana zamani kuma na iya rubutu hagu da dama hakan yasa kafin nafara waka rubutu nafarayi kuma dashi ne akafi sanina. Na rubuta fina finai, Documentaries, Articles, Audio Visuals, voiceover, da sauran tallace tallace na TV da Radio.
Yau naje neman Aure ance baza abaniba sabida ina waka toh so kuke inzama shararren mazinaci? Wa iyazu billahi.
Ko so kuke na amsa tayin gida da mota da wasu gurbatattu sukeyi man nacewa inshiga kungiyarsu ta yan madigo da luwa?
Acikin Al Qur’ani akwai mata guda goma 17 da Allah ya haramta a auresu, shin nima ina daga cikin jerin wayanda Allah ya haramta a aura kamar wayancen matan 17?
Allah ne yazabaman waka tunda kafin nayita nayi sana’o’i dayawa kuma ina alfahari da WAKA aure kuma na hakura dashi tunda ba wajibi baneba sunnah ce hakkokinsa ne wajibi.
Ku kuma masu yiman gori akan aure shin zaku iya bani auren kannenku ko yayanku a matsayina na mawaki? Idan zaku bani toh sai muduba compatibility a Qur’an 24 Nur: V 26 idan mundace da juna.
Kamata yayi atambayeni addini idan ban iyaba sai ahanani aure idan kuma sana’ata ce ta waka ke ba’aso toh nayi karatun zamani dana addini kubani aiki ko kubani jari na iya kasuwanci.
Anyiman gorin aure, anyiman gorin haihuwa, an yanke zumunta dani sabida banda kudi. Shin miyasa har yau babu wanda yataba yiman gori akan banida ilimi ko rashin ibada?
Wasu daga cikin mutane ba addini da ilimi bane agabansu burinsu kawai su aibataka.
Ina KALUBALANTAR duk wani ko wata wanda yakeda wani abu na aibu akaina da kada ya rufaman asiri yafito ya fallasani.
Ni musulmi ne cikakke mai bin Allah kuma mai bin Annabi Muhammadu (S. A. W) kuma waka ce sana’ata dukda ba akanta kawai na dogaraba.
Zaharaddeen A. Abdallah +2348036176288
zaabigchief@gmail.com Please 🙏 share, like and comment or suggest.