Tsohon shugaban Jami’ar Ibadan Farfesa Olufemi Bamiro ya bayyana cewar yawan Malaman dake akwai a Jami’o’in Najeriya ga Ɗalubai yayi kaɗan.
Bamiro ya ce hakan yana ɗaya daga dalilan da suka sanya babu wata Jami’a da aka sanya a jerin Jami’o’i 100 da suka yi fice a duniya.
Tsohon Shugaban Jami’ar ya bayyana haka a lokacin da ya gabatar da wata Lakca da Ƙungiyar Injiniyoyi reshen Jahar Ibadan ta shirya domin girmama Emmanuel Oladeji, Wanda ake ganin yana ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa fannin Injiniya na zamani na Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan sanda a Jigawa sun kama mutane 2 da laifin satar shanu
Bamiro ya ce Jami’o’in Najeriya basu da yawan ɗalubai, kuma suna da Ƙarancin Ma’aikata.
Tsohon shugaban Jami’ar ya jaddada cewa Jami’o’in Najeriya an bar su a baya sosai.
A cewar sa wannan dalilan ne suka sanya Malamai da dama basu san dukkanin ɗaliban su ba.
Bamiro yace baya ga yawan ɗalibai ga Malamai, yawan kayayyakin aiki, da yawan kwasa-kwasan da aka tantance, da ƙwazon ɗalubai, bada gudunmawa ga tattalin arziki, sune wanda ake amfani dasu wajen sanya jami’a daga cikin manya a faɗin duniya.