Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara yunkurin dakatar da ficewar mambobinta zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kebbi.
A jiya ne jam’iyyar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki da aka kira domin sasantawa da ‘ya’yan da aka tsammanin ba’a damawa dasu, domin dakatar da yunkurina su na sauya sheka.
Kwanan nan ne wasu jiga-jigan jam’iyyar APC suka dunguma zuwa PDP saboda wasu dalilai. Jam’iyyar ta rasa Sanata Adamu Aliero da Dokta Yahaya Abdullahi da kuma dan majalisar wakilai, Barista Mohammed Bello Yakubu (Relisco), Mohammed Umar Jega da Abdullahi Zumbo.
‘Yan majalisar dokokin jihar, Habibu Labbo, Ismaila Bui da Mohammed Buhari Aliero, sun fice daga jam’iyyar suma.
Da yake jawabi yayin taron mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a shiyyar (Arewa maso yamma), Salisu Lukman, ya ce taron an yi shi ne da nufin magance korafe-korafen jiga-jigan jam’iyyar a jihar.
“Duk da sauya sheka da jam’iyyar ta samu, har yanzu ina da kwarin gwiwar cewa APC ce jam’iyyar da za ta lashe zabe a 2023. Ina iya ganin hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar na ci gaba da habaka kuma hakan na nuni da samun gagarumar nasara a karshe,” inji shi.
Ya kara da cewa jam’iyyar na bukatar dukkanin mambobin ta da su samu nasara a 2023, inda ya bayyana cewa, an yi taron ne domin jin ta bakin dukkanin ‘ya’yan jam’iiyar, da suka koka don samun mafita a matakin kasa..
A wani labarin kuma na daban.
Tsigewa: Kotu Za Ta Fayyace Makomar Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo A Yau
Wata babbar kotu da ke zamanta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a yau, za ta fayyace makomar mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan, wanda ke fuskantar barazanar tsige shi daga wasu ‘yan majalisar dokokin jihar.
Mai shari’a Akintola na babbar kotun Ring Road 7, a jiya, ya dage sauraren karar har zuwa yau.
Ya ce, “Hukuncin da aka so yankewa tun farko zia kar har zuwa gobe (yau).”
Hakan ya biyo bayan gazawar Cif Afolabi Fashanu (SAN), lauyan mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, ya kasa gabatar da martani kan korafin da shugaban majalisar, magatakarda da kuma majalisar dokokin jihar Oyo suka shigar kan batun tsige shi a cikin jihar.
Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa ‘yan majalisa hudu daga cikin 33 a majalisar dokokin jihar Oyo a ranar 15 ga watan Yunin 2022 sun kawo zarge-zarge biyar a kan mataimakin gwamnan.
Zarge-zargen sun hada da, “rashin da’a, sabawa dokokin aikin ofis, watsi da ofis da aikin hukuma da rashin biyayya da sauran laifuka.”