Gwamnatin tarayya ta ce akalla yan Najeriya miliyan 67 ne suka yi rajistar lambar shaidar kasa, NIN, wadda ita ce tushen ci gaban tattalin arziki da tsaron kasa.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Malam Isa Pantami ne ya bayyana hakan a birnin Paris a wajen taron hadin gwiwar kasa da kasa na Najeriya da aka gudanar wanda wani bangare ne na taron zaman lafiya na birnin Paris din kasar Faransa.
Taron wanda ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ’yan kasuwa daga Najeriya da Faransa, an shirya shi ne domin nuna irin dimbin damarmakin kasuwanci da zuba jari a Najeriya.
Ya ce a halin yanzu an fi mayar da hankali kan matasa masu shekaru daga shekara daya zuwa 14, wajen ganin sun mallaki wannan lambar.
Ministan ya ce gwamnati ta mayar da hankali ga lambar ta NIN ne saboda ita ce ginshikin ci gaban tattalin arzikin kasa, da tabbatar da tsaron kasar da kuma kare masu zuba jari daga yan zamba da damfara.