Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce kudaden shiga da ke ci gaba da habbaka a baitul malin kasa a ‘yan kwanakin nan suna fitowa ne daga ɓangaren da ba na mai da iskar gas ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Josephine Ademu, jami’ar yada labarai da hulda da jama’a ta ma’aikatar kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire ta tarayya ta fitar ranar Juma’a a Abuja.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a taron kasa da kasa na shekara-shekara karo na 51 na kungiyar (NSCHE) a ranar Alhamis a Legas.
Osinbajo wanda ya samu wakilcin Dakta Ogbonnaya Onu, ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire ya yi nuni da cewa gwamnatin tarayya ta yi aiki tukuru domin ganin kasar ta samu ci gaba ta fuskar tattalin arziki.
A cewarsa, hakan na faruwa ne saboda yadda kasashen duniya da suka ci gaba da fasahar kere-kere suka sauya sheka zuwa makamashi mai tsafta da sabunta su.
Comments 1