Kimanin ‘yayan jam’iyyu daban-daban hars guda 546 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Mallam Madori ta jihar Jigawa.
Daily Post ra ruwaito cewa, Shugaban karamar hukumar, Malam Usaini Umar BK ne ya bayyana haka a lokacin da yake karbar wadanda suka sauya sheka a Malam-Madori ranar Laraba.
Ya ce sama da magoya bayan jam’iyyun adawa 546 ne suka bar jam’iyyarsu suka koma APC gabanin zaben 2023.
KARANYA WANNAN LABARIN: Na Siyar da Motar Maigidana Don Na Gudu Na Bar Najeriya —Wanda Ake Zargi
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Jigawa ta arewa maso gabas, Alhaji Ango Mallam-Madori ya yi maraba da wadanda suka sauya sheka daga jam’iyun nasu zuwa jam’iya mai mulki, inda ya kuma yi alkawarin daukar su kamar sauran ‘yayan jam’iyyar.
Ya bukace su da su hada kan su, su yi kokarin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban masu sauya shekar Malam Muhammad Mai Yarbawa ya ce sun bar jam’iyyarsu ne saboda rashin tsari da kuma rashin cika alkawari.
Ya kuma bada tabbacin yin aiki tukuru domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a babban zabe mai zuwa.
A WANI LABARIN KUMA: Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Fashi 3 A Jihar Benue
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami da miyagun kwayoyi da kuma kasancewa mambobin kungiyoyin asiri.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.