Yayi Sauri Peter Obi zama Shugaban Ƙasa, kawai dai zai yi Suna ne yanzu — Inji Babangida Aliyu
Tsohon Gwamnan Jahar Niger Babangida Aliyu yayi imanin cewa Dan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar Labour Party yayi garaje akan ya zama Shugaban Ƙasar Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: An yi gunduwa-gunduwa tare da cusa gawar wata mata acikin buhu a Abuja
Babangida yace Obi zai iya zama Shugaban Ƙasa a Shekarar 2027, ko 2031, amma 2023, yayi sauri, domin ƴan Najeriya mai yiwuwa basu shirya zaɓar tsohon Gwamnan Jahar Anambra a matsayin Shugaban Ƙasa.
Ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa a gidan Talabijin na Channels a cikin Shirin Siyasar mu.
A cewar sa, mutane da dama a Jam’iyyar PDP sun yi ta neman Obi ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa na Atiku Abubakar.
Yace “Peter Obi abokina ne na ƙwarai, Kuma shine tsohon Mamba na a Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya,” Inji Aliyu.
“Takarar sa musamman akan abinda ya shafi Shugabancin Ƙasa, kawai yanzu dai yayi suna. Amma zai iya samu nasara a zaɓen 2027, 2031. Amma shekarar 2023 yayi sauri.
Comments 1