An kashe shugabar Matan jam’iyyar Labour Party (LP) a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, Victoria Chintex har lahira.
Sakataren yada labarai na Jam’iyyar a shiyyar Kudancin Kaduna, Edward Buju, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata.
Buju ya ce mijin Chintex ya samu rauni a harin kuma a halin yanzu yana karbar magani a wani asibiti.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Jam’iyyar Labour ta Kudancin Kaduna (Zone 3) ta mika ta’aziyya ga shugaban jam’iyyar tare da jiga-jigan ta na karamar hukumar Kaura, bisa rasuwar uwarmu da ‘yar uwarmu, Misis Victoria Chintex, shugabar mata ta karamar hukumar Kaura wadda ta rasu.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka kashe ta a jiya (Litinin) a gidanta da ke Kaura.
“Bugu da ƙari, yayin da muke jiran shirye-shiryen binne iyali, jam’iyyar Labour Party ta Zone 3 za ta tallafa wa danginta.
“A madadin dan takarar shugaban kasa, Peter Obi; dan takarar mu na gwamna a jihar Kaduna, Jonathan Asake; Dan takarar sanatan jam’iyyar a shiyyar Kudancin Kaduna, Mike Auta, muna kira ga al’ummar karamar hukumar Kaura da su kasance masu bin doka da oda domin Ubangiji zai saka mata.”
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna bai mayar da martani ba lokacin da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa kan wannan lamarin.
A Wani Labarin Kuma Dalilin Da Yasa Yan Daba Suke Kai Hari Tare Da Kona Ofisoshin INEC — Shehu Sani
Tsohon dan majalisar dattawa na Kaduna, Shehu Sani ya bayyana cewa dalilin da ya sa masu aikata laifuka ke kai hari tare da kona ofisoshi da sauran cibiyoyin hukumar zabe ta kasa (INEC) shi ne yin zagon kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa, ‘Yan bindiga sun yi ta kai hare-hare tare da kona kayayyaki a ofisohin hukumar INEC a fadin kasar nan, musamman a yankin Kudu maso Gabas.