A ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba ne aka sha shagalin auren fitacciyar jarumar Kannywood Halima Atete.
Cincirindon jarumai mata da maza sun je bikinta wanda aka sha shagulgula iri-iri cike da al’adun Kanuri wato mutanen Maiduguri.
KU KARANTA: Budurwa ta tashi saurayi a Twitter bayan ya ce ya shirya aure amma be samu matar aure ba
A hotunanta da su ka bayyana, an ga yadda jarumar taci kurus ta sanya kayan alfarma kuwa ta dauki kwalliyar kece raini.
Babu wata alamar makusa, kuma ko da wakilin Dimokuradiyya be je bikin ba amma ko da gani wurin ya dauki kamshi kasancewar haka al’adar mutanen Maiduguri take.
Saidai a dayan bangaren, an samu wadanda su ka kushe ta. A wata wallafa da wata matashiyar tayi a wani rukunin Facebook mai suna Sirrin ‘Ya Mace, ta shaida yadda jarumar ta sanya mayafin da ya bule.
Ta yi zargin cewa ko dai kuda ne ya makale a jikin mayafin. Duk da dai da wasa tayi wallafar amma ta sha caccaka da zagi ta uwa ta uba a wallafar.
Nan da nan ‘yan gani-kashenin jarumar su ka yi mata tatas har da masu wallafa hotonta su na sukarta inda su ka ce ita kanta sai a hankali.
Shekarar da ta gabata warhaka muna shagalin aurenmu, Matashi na makokin rasuwar matarsa
Wani dan Najeriya mai suna Mustapha Ahmad Junaid ya koka bayan rasuwar matarsa Fatim Zarah, a ranar da ya kamata su cika shekara daya da aure, LIB ta ruwaito.
Zahra wacce ta rasu da juna biyu a ranar Laraba, 7 ga watan Satumban 2022, bayan watanni 8 da aurensu.
Mustapha ya auri Zahra ranar 26 ga watan Nuwamban 2021 a Jihar Sokoto. Ya yi wallafa a Twitter ranar 26 ga watan Nuwamban inda yace har yau yana fama da radadin mutuwar Zarah.