Yayin da Rikicin PDP ke ƙara ta’azzara, Wike, Ortom, Makinde sun sake ganawa a Landan
Yayin da rikicin jam’iyyar PDP ke kara taɓarɓarewa, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, da takwarorinsa na jihar Benue da Oyo, Samuel Ortom da Seyi Makinde sun sake ganawa a birnin Landan na kasar Birtaniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: ADC ta dakatar da Ɗan Takararta na Shugaban Ƙasa, Kachikwu
Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayanin taron na ranar Juma’a ba, masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin yana da alaka da rikicin da ke cikin jam’iyyar PDP
Idan za’a iya tunawa akwai yunkurin sasanta Wike da Atiku Abubakar, wanda dangantakarsu ta yi tsami bayan zaben fidda gwani na PDP ya ci gaba da yin wuya.
Vanguard ta ruwaito cewa Makinde wanda ke hutun ƙarshen shekara tun a taron da ya gabata, Wike ne ya fara haduwa da shi, yayin da Ortom wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Amurka ya tsaya domin taron.
An tattaro cewa, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu na iya ganawa da Gwamnonin PDP a kasar Ingila domin kammala taron da ya gabata.
Ku tuna cewa Gwamna Seyi Makinde da takwaransa na jihar Abia, Dokta Okezie Ikpeazu da sauran jiga-jigan PDP daga sansanin Gwamna Wike sun gana da Asiwaju a Landan a ranar 23 ga watan Agusta.
DAILY POST ta bada rahoton cewa gazawar Gwamna Wike na samun tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar a 2023 ya ci gaba da wargaza jam’iyyar adawa ta PDP.
Wike ya sha kaye a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja ranar 28 ga watan Mayu a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Har ila yau fatansa na fitowa takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar ya ci tura lokacin da Atiku ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa.
Lamarin dai ya ci gaba da ruruwa daga sansanin Gwamna Wike yayin da ya sha alwashin tabbatar da cewa Atiku ya sha kaye a zabe mai zuwa.
A wani labarin kuma: Buhari ya kara Kuɗin Tafiye-tafiye ga Ministoci, Manyan Sakatarori da sauran su
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da kara wa jami’an gwamnati da ma’aikata alawus alawus-alawus na yawon bude ido (DTAs).
Ministoci da sakatarorin dindindin da ma’aikatan gwamnati a mataki na daya zuwa 17 za su ci gajiyar wannan karin.