By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta tace za ta aiwatar da duk wasu dokokin da suka haramta amfani da kayan wasa na wuta a lokacin bikin Yuletide.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Ari Ali ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya rabawa manema labarai ranar Alhamis a garin Warri.
Ali ya gargadi iyaye dasu tabbatar da cewa unguwanninsu basu karya dokar ba kafin lokacin bukukuwa da kuma bayan bukukuwan.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma gargadi ‘yan kasuwar dake mu’amala tare da sayar da kayan wasan wuta dasu daina sayar da kayayyakin a halin yanzu.
Har yanzu dokar hana amfani da kayan wasan wuta na ci gaba da aiki kuma hukumar za ta aiwatar da duk wasu dokokin da suka haramta amfani da kayan wasan wuta kamar ‘knock-out’, ‘banger’ da sauransu musamman a wannan lokacin na Yuletide.
“An kuma shawarci iyaye da su ja-goranci ‘ya’yansu da unguwannin su da su daina amfani dasu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “An kuma gargadi masu siyar da irin wadannan kayayyaki da su janye daga siyar da wadannan kayayyakin domin duk wanda aka kama za a gurfanar da shi gaban kotu,” in ji CP.
Sai dai Ali, ya umurci dukkan kwamandojin yankin, jami’an ‘yan sanda na yanki da kuma kwamandojin dabarun yaki da su tabbatar da bin doka da oda na haramcin amfani da kayan wasan wuta a yankunansu.sannan ya kuma ce an tura jami’an ‘yan sanda a boye domin kamo duk wanda ya karya doka.
Kazalika ya kuma bai wa mazauna yankin tabbacin tsaron lafiyarsu a kowani lokaci, inda ya bukace su da su ci gaba da baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro bayanai masu amfani domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.