• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Tuesday, September 26, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Uncategorized

Yunkurin Fara Ba Da Ilimi Kyauta A Jihar Kano, Gwamna Ganduje Ya Ƙarfafa Hukumar Ilimi Matakin Farko

Mustapha Haruna Khalifa by Mustapha Haruna Khalifa
August 7, 2019
in Uncategorized
Reading Time: 2 mins read
0 0
0
0
SHARES
3
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA Baahi Abdullahi El-bash:-

A cigaba da yunƙurin da ake na tabbatar da wajabcin Ilimi da ba da shi kyauta tun daga firamare har zuwa babbar sakandire, kamar yadda ya alƙawarta, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya ƙarfafa hukumar Ilimi matakin farko ta Jiha (SUBEB) ta hanyar naɗa Malam Baffa Saleh Muhammad a matsayin sabon sakataren hukumar.

Malam Baffa Saleh Muhammad, tsohon malamin makaranta ne wanda ya fara aikin koyarwa a makarantar sakandiren koyar da harkokin kasuwanci ta garin Wudil a shekarar (1985). Har ya kai matsayin Daraktan kula da makarantu a hukumar ilimi matakin farko (SUBEB). Ya kuma riƙe muƙamin shugaban hukumar na riƙon ƙwarya har zuwa lokacin da mai girma gwamna ya tabbatar da naɗin Dakta Ɗanlami Hayyo a matsayin cikakken shugaban hukumar.

Kafin nan kuma, ya taɓa riƙe mukamai daban-daban a fannin Ilimi. Ya taba zama babban malami, matemakin shugaban makarantar sakandire, shugaban makarantar sakandire har sau hudu daga (1991) zuwa (2000). Ya kuma taɓa zama sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar Ajingi daga (2000) zuwa (2001). Sannan kuma ya taɓa zama jami’i mai sanya ido kan makarantun firamare na Jiha daga (2001) zuwa (2004). Da sauran muƙamai da ya taɓa riƙe a fannin Ilimi.

Gwamna Ganduje ya bayyana cewa zaɓo mutum tsohon hannu wanda ya taba riƙe muƙamai daban-daban a harkar Ilimi irin wannan, zai taimaka matuƙa wajen cimma muradun da aka sanya a gaba ciki kuwa har da samun nasarar zamanantar da karatun allo da kuma fara aiwatar da shirin wajiabcin Ilimi da kuma ba da shi kyauta a Jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya yi imanin ƙarfafa ma’aikatun Ilimi, shi ne ginshiƙin cimma muradun da ake da su. Shi ya sa ma ya yanke shawarar naɗa sabon sakataren wannan hukuma ta (SUBEB).

Takardar wannan naɗi ta fito ne daga hannun sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ta hannun sakataren dindindin kan harkokin nazari da bincike da harkokin siyasa (REPA). Darakta Bilkisu Shehu Maimota, ta yi cikakken bayani kan yadda gwamna Ganduje ya amince da wannan naɗi na Malam Muhammad a matsayin sakataren (SUBEB).

An karanta takardar kamar haka “a yunƙurin wannan gwamnati na bunkasa hukumomin gwamnati da ma’aikatu kan gudanar da ayyuka yadda su ka kamata da samar da cigaba mai ɗorewa zuwa gaba, mai girma zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, (OFR) ya amince da naɗinka a matsayin sabon sakataren hukumar ilimi matakin farko (SUBEB) kuma naɗin naka ya fara ran 21 ga watan Yuli, 2019.

Ta cigaɓa da ƙarin bayani cewa “an kuma zaɓo ka ne an baka wannan muƙami kan la’akari da cancantarka da sahihancin takardunka da gaskiyarka da ƙwarewa da gogewarka ta aiki da hazaƙarka da kishinka gami da juriya da jajircewarka da biyayyarka da kuma irin gudunmawar da ka bayar wajen cigaban Jiharmu abar alfaharinmu.

Wannan naɗi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamna Ganduje ya himmatu wajen tabbatar da fara aiwatar da shirin wajabcin Ilimi da kuma ba da shi kyauta tun daga firamare har zuwa babbar sakandire a Jihar Kano.

Previous Post

Ofishin Jakadancin Amurka A Najeriya Ya Karrama Ali Nuhu

Next Post

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a safiyar yau ya tafi kasar Saudiyya don yin aikin hajjin Bana

Next Post

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a safiyar yau ya tafi kasar Saudiyya don yin aikin hajjin Bana

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2705 shares
    Share 1082 Tweet 676
  • Batun Dakatar Da Opay Da Palmpay, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance

    2411 shares
    Share 964 Tweet 603
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    2198 shares
    Share 879 Tweet 550
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    2078 shares
    Share 831 Tweet 520
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1503 shares
    Share 601 Tweet 376
Hukumar INEC Ta Sabunta Dan Dalinta Na Duba  Sakamako

INEC ta Sanya Ranakun Gudanar da Zabukan Gwamnoni a Wasu Jihohi 2

September 26, 2023
Mutum 204 Hatsarin Mota Ya Kashe A Bauchi Cikin Watanni 9-Road Safety

Mutum 204 Hatsarin Mota Ya Kashe A Bauchi Cikin Watanni 9-Road Safety

September 26, 2023
Nijar: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Tinubu da ECOWAS Su Binciko Zabin Siyasa da Diflomasiyya

Akpabio Ya Nemi Hadin Kai Tsakanin ‘Yan Majalisa Don Tunkarar Kalubalen Najeriya

September 26, 2023
Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Tantance Sabon Gwamnan CBN da Wasu Mutane Hudu

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Tantance Sabon Gwamnan CBN da Wasu Mutane Hudu

September 26, 2023
Ku Tabbatar Kunyi Aiki Tare Da Kowane Dan Jam’iyya A Cikin Mulkinku-Tinubu Ga Sabbin Shugabannin APC

Tinubu Ya Taya Yan Najeriya Murnar Watan Maulud Ya Bukaci Su Taya Kasar Da Addu’oi

September 26, 2023
Gwamnatin Jahar Ogun Ta Hana Bukukuwan Ranar Samun Yancin Kai

Gwamnatin Jahar Ogun Ta Hana Bukukuwan Ranar Samun Yancin Kai

September 26, 2023
Hukumar INEC Ta Sabunta Dan Dalinta Na Duba  Sakamako
Siyasa

INEC ta Sanya Ranakun Gudanar da Zabukan Gwamnoni a Wasu Jihohi 2

September 26, 2023
Mutum 204 Hatsarin Mota Ya Kashe A Bauchi Cikin Watanni 9-Road Safety
Labarai

Mutum 204 Hatsarin Mota Ya Kashe A Bauchi Cikin Watanni 9-Road Safety

September 26, 2023
Nijar: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Tinubu da ECOWAS Su Binciko Zabin Siyasa da Diflomasiyya
Labarai

Akpabio Ya Nemi Hadin Kai Tsakanin ‘Yan Majalisa Don Tunkarar Kalubalen Najeriya

September 26, 2023
Hukumar INEC Ta Sabunta Dan Dalinta Na Duba  Sakamako

INEC ta Sanya Ranakun Gudanar da Zabukan Gwamnoni a Wasu Jihohi 2

September 26, 2023
Mutum 204 Hatsarin Mota Ya Kashe A Bauchi Cikin Watanni 9-Road Safety

Mutum 204 Hatsarin Mota Ya Kashe A Bauchi Cikin Watanni 9-Road Safety

September 26, 2023
Nijar: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Tinubu da ECOWAS Su Binciko Zabin Siyasa da Diflomasiyya

Akpabio Ya Nemi Hadin Kai Tsakanin ‘Yan Majalisa Don Tunkarar Kalubalen Najeriya

September 26, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • INEC ta Sanya Ranakun Gudanar da Zabukan Gwamnoni a Wasu Jihohi 2
  • Mutum 204 Hatsarin Mota Ya Kashe A Bauchi Cikin Watanni 9-Road Safety
  • Akpabio Ya Nemi Hadin Kai Tsakanin ‘Yan Majalisa Don Tunkarar Kalubalen Najeriya

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In