Gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) za su gana a ranar Talata.
Hakan ya faru ne sakamakon yajin aikin gargadi na wata daya da kungiyar ta shiga.
Yayin da yake bayyana yajin aikin, Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar ASUU, ya zargi gwamnati da gazawa wajen biyan bukatun malamai.
Bukatun sun hada da farfado da jami’o’in gwamnati, samun alawus alawus a fannin ilimi, amfani da tsarin Transparency Accountability Solution (UTAS) a Mai makon (IPPIS) sake tattaunawa kan yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya na 2009.
A ranar Litinin, mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, Charles Akpan, ya tabbatar da cewa Sanata Chris Ngige, zai gana da shugabannin kungiyar da sauran hukumomin gwamnati da suka shafi shiga yajin aikin.
An shirya taron ne a ranar Talata, da karfe 1 na rana. a dakin taro na ministan.