Hukumomin jami’ar UNIBEN a ranar Laraba sun bayyana dakatar da dukkanin membobin kungiyoyin dalibai dake jami’ar.
Kakakin jami’ar, Dr Benedicta Ehanire, shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa day a fitar a Benin, inda ya ce za a kafa kwamiti da zai ci gaba da lura da al’amuran kungiyar.
Ehanire ya ce hukumar jami’ar ta dakatar da su ne domin dakile yunkurin tayar da hargitsi da dawo da doka da oda sakamakon yunkurin zanga-zanga da kungiyar ta yi shirin yi akan sauyin tsarin karatu da aka samu a jami’ar.
Hukumar jami’ar ta ce zanga-zangar wani yunkuri ne kawai na tayar da hargitsi a cikin makarantar.
“hukumar jami’ar a karkashin shubabanta, Farfesa Lilian Salami, na kokarin bayar da dukkanin abubuwan bukata, wanda ya hada da ruwa da wutar lantarki, da sauran kayayyakin karatu”.
Ya ci gaba da cewa; “mun kuma kulle asusun bankin kungiyar, sannan mun kulle sakatariyar kungiyar. Dukkanin membobin kungiyar da shugabanninta su dawo da shaidarsu zuwa ga shugaban tsaron jami’ar da gaggawa”, ya tabbatar.