Sabon Sakataren Jam’iyar PDP na Ƙasa Sanata Samuel Anyanwu yace dalilin samun nasarar sa, shine ya haɗa hannu da sauran mambobin kwamitin amintattu na PDP, domin tabbatar dacewa an ceto Najeriya daga rashin iya mulki na Jam’iyyar APC.
Anyanwu ya bada tabbacin cewa matsayin sa na Sakataren Jam’iyar na Ƙasa, ba yana nufin farautar wani ba.
Yace “a yanzu jamiyyar mu bazata taɓa yarda ta faɗi ba, dole muyi abinda zamu iya na ganin samun zaman lafiya. Kuma hakan zai fara ne ta hanyar kamatan tawa, da sasanci a tsakanin mambobin jami’iyyar a faɗin Najeriya.

KARANTA WANNAN LABARIN: Kasar Iran Taki Amincewa Da Damuwar Kasashen Yammacin Turai Game Da Shirinta Na Makaman nukiliya
Anyanwu ya bayyana haka a ranar Litinin a cikin wata sanarwa da mai bashi shawara akan kafafen yaɗa labaru Ikenna Onuoha ya fitar.
Yace ƙudirin shi, shine na ganin an haɗa kan kowa da kowa, maimakon farautar wani.
Ya buƙaci magoya bayan Jam’iyyar PDP dasu cigaba da siyasa domin samo ƙarin mambobin jami’iyyar, yana mai basu tabbacin ƙudirin shi na haɗa kai da abokanan aiki, domin samun nasarar jamiyyar a shekarar 2023.