Shuwagabannin Siyasa dana Addini a Jahar Kano, sun bada tabbacin goyon bayan su ga Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello a Babban Zaɓe mai zuwa na Shekarar 2023.
Shuwagabannin sun shaidawa Gwamna Yahaya Bello haka a ranar Lahadi a Abuja suna mai bayyana cewa sun tabbata cewa Yahaya Bello zai iya gyara Najeriya.
Tawagar sun kuma sha alwashin su na cigaba da yin biyayya a lokacin da suka ziyarci Yahaya Bello, a matsayin shi na cikakken masoyin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, kuma a shirye suke su bada goyon bayan da yake buƙata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fim Din Da Ya da ce da Addinin Mu, Shi Muka Sa Agaba~Safyanu Lawal Kabo
Shugaban Tawagar Alhaji Shu’aibu Idris, yace tun Shekarar 2003 suke bada goyon bayan su ga Buhari, tare bada tabbacin bayar da irin wannan goyon baya ga Gwamna Yahaya Bello domin ya gaji Buhari bayan ya kammala wa’adin mulkin sa.
Idris yace suna goyon bayan Yahaya Bello ne sabudda yanda ya samu nasara a mulkin Jahar Kogi, kuma wannan ya sanya suke son suga an samu irin shi a matakin Tarayya.
“Wannan taro ne na mutanen Jahar Kano daga ɓangarori daban-daban na rayuwa, kuma dukkanin mu munzo domin abu guda ɗaya, shine mu samarwa Najeriya makoma daga gare ka.
“Jahar Kano tuni ta kasance wadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yake samun nasarar lashewa tun shekarar 2003, har zuwa yanzu, har kuma gobe.
“Muna son mu tabbatar maka dacewa irin soyayyar da muke da’ita ga Shugaban Muhammadu Buhari idan ya kammala wa’adin mulkin sa, zamu damƙa ta a gareka.
“Ina son in tabbatar maka dacewa mun ba Shugaban Ƙasa ƙuri’a Miliyan ɗari biyu, yanzu kuma yawan mu ya ƙaru, muna tabbatar maka da cewa zamu baka fiye da ƙuri’a Miliyan ɗari biyu.
“Mun tantance ƙwazon ka, kuma munga cewa kayi ƙoƙari matuƙa, kuma kaine mutumen daya dace ya ciyar da Najeriya a matakin gaba.
“Muna son mu tayaka murna akan amincewa da Janar Ibrahim Babangida mai ritaya yayi akan ka, a lokacin da yace, Najeriya a yanzu tana buƙatar matashi mai tsoron Allah, mai maida hankali, wanda yasan abubuwa da dama.
“Idan na duba sai ince Janar Ibrahim Babangida dama ya faɗi suna, kuma duk da bai faɗi suna ba, dukkanin abubuwan daya faɗa sun nuna kai ne.
“Da irin wannan amincewa da cikakken ɗan ƙasa yayi a gareka kamar Janar Ibrahim Babangida, muna da tabbacin Allah zai kasance a tare damu,” inji Idris.
Dayake maida jawabi, Gwamna Yahaya Bello ya bayyana jindaɗin sa na yadda suka gano irin nasarorin daya cimmawa a Jahar Kogi, da kuma goyon bayan su.
Gwamnan yace kamar yadda kowacce ƙungiya da ƴan Najeriya ke kira a gareshi daya fito takarar Shugaban Ƙasa, bazai basu kunya ba.
Yace a matsayin shi na masoyi ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yana cikin wata ƙungiya dake da manufar kawo cigaba a Najeriya.
“Ina son in gode maku akan wannan yabawa da kuka yi akan cigaban dana cimmawa.
“Kun kasance cikakkun masoyan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga Jahar Kano wanda ina ɗaya daga cikin mamba.
“Don haka kunzo kuga abinda ɗaya daga cikin ku yayi, domin yabawa akan nasarorin da muka cimmawa ga Al’ummar Jahar Kogi,” Inji Bello