Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar APC a Jahar Ekiti kuma Gwamnan Jahar Jigawa Abubakar Badaru, ya bayyana a ranar Laraba cewa mambobin jami’iyyar wanda zasuyi zaɓen fidda Gwani a faɗin Mazaɓu 177 na Jahar zasu bi layine a bayan fastar ɗan takarar da suke so.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: ku kai tikitin takarar Shugaban Ƙasa a Arewa, wata ƙungiya tayi kira ga PDP
Badaru yace masu ruwa da tsaki da ƴan takara sun cimma matsayar cewa sai mamba mai rajista cikakkiya za’a bashi dama yayi zaɓe a zaɓen dazai gudana a Jahar a ranar Alhamis.
Dayake jawabi tunda Farko, Badaru yace Ƴan sanda da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta sun bada tabbacin cewa zasu bada cikakkiyar kulawa da wuraren zaɓen.
Shugaban Kwamitin wanda yayi jawabi a Ado Ekiti, Babban Birnin Jahar a lokacin taron masu ruwa da tsaki daya samu halartar ƴan takara da Shuwagabannin Jam’iyyar, ya bada tabbacin gudanar da zaɓen fidda gwani na adalci, yana mai cewa babu wani ɗan takara da za’a cuta.
Ƴan takara da suka halarta sun ƙunshi Sanata Opeyemi Bamidele, da tsohon Ministan Ayyuka Sanata Dayo Adeyeye, da ɗan majalisar wakilai Femi Bamisile, da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Biodun Oyebanji da sauran su.