Sufeto-Janar na Ƴan sandan Ƙasar nan Usman Alƙali Baba ya bada umarni ga jami’an ƴan sanda dubu 34,587 gami da jirage masu saukar angulu uku da suje Jahar Anambra, gabanin zaɓen Gwamna mai zuwa domin tabbatar da cewa anyi sahihin zaɓe.
Mai Magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan na Ƙasa Frank Mba ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, a lokacin wani taro na manyan jami’an ƴan sanda karo na biyu wanda ya fara daga muƙamin kwamishina zuwa sama a Abuja.
Sauran kayayyakin da aka tura a zaɓen Gwamnan Anambra da aka sanya ranar 6 ga watan Nuwamba na Shekarar 2021, ya haɗa da jirage da ɓangaren dabbobi da sauran su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wallahi zan iya sadaukar da kujera ta domin a samu tsaro a Katsina — Cewar Sarkin Katsina
Sufeto-Janar ɗin ya bayyana cewar daga cikin wani ɓangare na samar da kyakkyawan yanayi da zai tabbatar da zaɓe cikin kwanciyar hankali, rundunar ta gudanar wani horaswa ta sabbin dabaru akan matsalolin zaɓe, gami da tura jami’an tsaro a Jahar.
IG Alƙali ya ɓukaci al’umma dasu baiwa ƴan sanda haɗin kai a wuraren su , domin tabbatar da lafiyar su a Ƙasa baki ɗaya.