Hukumar Kula da gidan gyaran aƙida ta Kasa, ta ƙaryata rahoton dake cewa anyi wani shirin sanya ƴan gidan yari, daa cikin waɗanda zasu yi zaɓen Gwamna a Jahar Anambra.
Mai Magana da Yawun Hukumar Francis Enobore yayi kira ga ƴan Najeriya dasu jefar da wannan rahoto daya fito daga Emma Powerful Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Ƴan Aware na IPOB.
Enobore ya bayyana haka a ranar Juma’a, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙarya da kuma karkatar da hankulan al’umma.

KARANTA WANNAN LABARIN: Zanga zangar adawa da zaben Iraqi ya rikiɗe zuwa Tarzoma
Yace “Hankalin Shuwagabancin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Aƙida ya kai akan wani labari daga cikin manyan jaridun Ƙasa, inda ake zargin cewa, ana ƙoƙarin shigar da ƴan gidan yari cikin jerin wanda zasu yi zabe, domin lalata darajar zaɓen Gwamna da aka sanya ranar 6 ga watan Nuwamba na shekarar 2021.
Wannan rahoton wani ƙarin mummunan aikin IPOB, na haifar da ƙiyayya da faɗa a tsakanin Al’umma, tana mai cewa Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa kaɗai ke gudanar da harkokin zaɓe a Ƙasar