Shugabannin addinin Kirista sama da 300 ne suka amince tare da yiwa tafiyar gwamna Obaseki amanna a karo na biyu.
Ƙungiyoyin sun bayyana cewa sun aminta da irin tsare-tsaren da gwamna yake dasu na ci gaban al’umma da kuma samar da ababan more rayuwar jama’ar jihar Edo.
Shugaban ƙungiyar Minded Ministers Association Rev. Dakta Sharp Okoro ya ce “Mun lura cewa kai ba gwamna bane mai yawan suturu, ka fi bari ayyukan da ka yi su gabatar da kai ko wane. Kuma ba zamu manta da irin gudunmawar da ka bawa addini ba”.
https://dimokuradiyya.com.ng/wasu-daga-cikin-gwamnonin-apc-na-goyon-bayana-har-yanzu-obaseki/
A nasa ɓangaren kuwa gwamna Obaseki ya ce “Bana so na faɗa fushin ubangiji da laifin zubar da jini wani a zaɓen da za a gudanar, ina buƙatar ku taya ni da addu’a a yi zaɓe lafiya ba tare da an salwantar da ran wani ba”.
Shi kuwa ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 19 ga watan Satumbar da za a gudanar, Ize-Iyamu ya maida hankalinsa ne ga kyautata rayuwar ma’aikatan jihar ta hanyar kawo sauye-sauye da zasu inganta rayuwarsu.