Gwamnan Jahar Delta Sanata Ifeanyi Okowa, yace samun nasarar gudanar da zaɓen shuwagabannin Jami’iyyar PDP, wani manuniya ce na ƙoƙarin Jam’iyyar wajen ceto Najeriya daga mummunan halin da take ciki.
Okowa ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a gidan Talabijin na Channels a Shirin “siyasar mu a yau” da aka yi dubi akan shi.

KARANTA WANNAN LABARIN: Tottenham Ta Sanar Da Daukan Antonio Conte, A Matsayin Sabon Kocin Ta
Yace Najeriya ta gaji da yawaitar matsalolin tsaro, da Tattalin Arziki dake addabar ƙasar, yace PDP ta hanyar samun nasarar zaɓen shuwagabannin ta, ta aika da saƙo mai mahimmanci ga ƴan Najeriya cewa ta damu da mummunan halin da ƙasar take ciki.
Gwamnan yace akwai buƙatar a sake ƙirƙirar wani fata ga ƴan Ƙasar, domin da yawan mutane sun rasa yardar su ga ƙasar.
Acewar sa “ya zuwa yau, bawai matasan mu kaɗai ba, har da ƴan Najeriya da dama na jin rashin jindaɗi akan yadda ƙasar take, da kuma yanayin da bai kamace mu ba.
Comments 1