Zaɓar Okowa bazai sanya PDP tayi nasara ba — Cewar CNG
Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa tace Gwamnan Jahar Delta Ifeanyi Okowa bazai baiwa Jam’iyyar PDP nasara a zaɓen Shugaban Ƙasa mai zuwa.
Okowa dai Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a PDP Alhaji Atiku Abubakar ya zaɓe shi a matsayin Abokin Takarar sa, wanda ya bayyana shi a matsayin Magaji na ƙwarai.
KARANTA WANNAN LABARIN: NDLEA ta kama Baron na Ƙwaya 10, da masu laifi 17,647 a cikin watanni 17
Da yake maida jawabi, Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Mr Abdul’aziz Suleiman a cikin wata sanarwar daya aike wa Jaridar PUNCH a ranar Litinin ya ƙalubalanci zaɓin PDP na Okowa, yana mai cewa domin dimokuradiyyar ta cigaba dole akwai matasa a cikin ta.
A cewar sa, Akanta kuma Ɗan Kasuwa Dr. Ibrahim Bello Dauda wanda yake daga yankin Arewa zaifi cancanta ya zama Abokin takarar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC.
Mai Taimako Ɗan Ƙabilar Kanuri Dauda wanda yake ɗan Asalin garin Gora, Ƙaramar Hukumar Shani, ta Jahar Borno yana ɗaya daga cikin masu ilmi da akayi imanin cewa zai iya zama Abokin takara.