Zaɓen 2023: INEC zata fara ɗaukar Ma’aikatan Wucin Gadi
A ci gaba da shirye-shiryen tunkarar Babban zaɓe na 2023, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasa INEC ta fara shirin ɗaukar ma’aikata na wucin gadi na babban zaben 2023.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba a shafinta na Facebook, ta bukaci masu sha’awa da masu cancanta su ziyarci adireshin yanar gizo da ta samar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Ya Sa Dole Jam’iyyar PDP Ta Mutunta Mu – Gwamnan Rivers
“Hukumar ta amince da sake buɗe manhajar INECPRES , ga wayar hannu wato- Mobile App na wayoyin Android da kuma yanar gizo ta hanyar amfani da laptop.
“Har zuwa wannan, tashar za ta kasance a buɗe ga masu neman cancanta don yin rajista na kowane nau’i na ma’aikatan Wucin gadi ga matakai na (SPO/PO/APO/RATECHS/RAC Managers) sai dai banda mai tattara sakamakon zaɓe na ƙaramar hukuma.
Sanarwar ta nuna cewa za’a buɗe adireshin yanar gizo a ranar Laraba 14 ga Satumba zuwa ranar 30 ga Nuwamba, 2022.
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, a makon da ya gabata ya ce za ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da na majalisun tarayya a ranar 20 ga watan Satumba. Hukumar zaben ta kuma ce za a fara yakin neman zabe a hukumance a watan Satumba.
A wani labarin kuma:Za’a dakatar da Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi kan karɓar Bashi a Jihar Neja
Kwamitin majalisar dokokin jihar Neja da ta kafa domin duba lamunin bayar da bashin kudaden kwangila ga kananan hukumomi ashirin da biyar ya ba da shawarar dakatar da shugabannin ƙananan Hukumomi goma sha biyar a jihar.
Majalisar ta dauki wannan mataki ne domin share fagen samun dama ga kwamitin ya gudanar da ayyukan shi yadda ya kamata.