Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Dr Mustapha Inuwa ya yi murabus ɗin ne donya fito a fafata da shi wajen neman Gwamnan jihar Katsina a zabe mai zuwa na 2023
Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Dr Mustapha Muhammad Inuwa ya rubuta takarar aje aikinsa na sakataren Gwamnatin jihar Katsina.
Sanarwar mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Afrilun 2022, Dr Mustapha Inuwa ya bayyana cewa ya aje akin ne don kashin kansa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da duminsa: Buhari, shugabannin hukumomin tsaro da ministoci sun gana a Aso rock
Za a iya tuna cewa Dr Mustapha Inuwa na daya daga cikin kusoshin Gwamnatin jihar Katsina, da kuma ya nuna sha’awarsa ta neman Gwamnan jihar a zabe mai zuwa na 2023.
Ko Jiya mataimakin Gwamnan jihar Katsina Q’S Mannir Yakubu ya aje mukaminsa na kwamishinan noma na jihar Katsina, domin neman kujerar Gwamnan jihar Katsina