Jam’iyyar APGA ta ƙara samun nasarar lashe ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa a zaɓen Gwamna da ake gudanarwa a halin yanzu.
Farfesa Chukuma Soludo Ɗan takarar APGA a zaɓen da ake gudanarwa, ya samu ƙuri’u 4,826, a yayinda ɗan takarar jam’iyar APC Andy Uba ya samu ƙuri’u 2,692, a sa’ilinda Ɗan takarar Jam’iyar PDP ya samu ƙuri’u 1,863.
A dukkanin sakamakon Zaɓen da aka sanar na ƙananan hukumomi 8, dukkanin su Ɗan takarar Jam’iya mai Mulki ya APGA shine ya lashe zaɓen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bukola Saraki Ya Soki Hukuncin Garƙame Majalisar dokokin jihar Filato
Ƙananan Hukumomin da aka sanar a cibiyar tattara sakamakon Zaɓe sun ƙunshi Orumba ta Kudu, da Orumba ta Arewa, da Njikoka, da Awka ta Kudu, da Onitsha ta Kudu, da Aguata, da Anaocha, gami da Anambra ta Gabas.
Soludo ya samu ƙuri’u dubu 60,988 a ƙananan hukumomi, sai Ozigbo nada ƙuri’u 24,972, inda ya bada tazarar dubu 36,016.
Uba shi kuma yana da 21, 505
Ga sakamakon kamar haka
Orumba Arewa
APC: 2692
APGA: 4826
PDP: 1863
Ƙaramar Hukumar Aguata
APC: 4773
APGA: 9,136
PDP: 3798
Ƙaramar Hukumar Njikoka
APC – 3216
APGA – 8803
PDP – 3409
Orumba ta Kudu
APC: 2,060
APGA: 4394
PDP: 1672
AWKA ta Kudu
APC – 2595
APGA – 12891
PDP – 5489
Onitsha ta Kudu
APC – 2050
APGA – 4281
PDP – 2253
Anambra ta Gabas
APC 2034
APGA: 9746
PDP: 1380
Ƙaramar Hukumar Anaocha
APC – 2085
APGA – 6911
PDP – 5,108
Comments 1