Da alama rikicin da ke addabar jam’iyyar APC a jihar Ekiti na daɗa kazancewa bayan da a ranar Juma’a shugabannin wani tsagin jam’iyyar a jihar su ka sanar da dakatar da gwamnan jihar, Kayode Fayemi daga jam’iyyar.
Kwamitin zartarwar tsagin jam’iyyar ne ya sanar da korar gwamnan bisa zarginsa da cin amanar jam’iyyar da irin rawar da gwamnan ya taka a zaben gwamnan jihar Edo na makon da ya gabata.
A wata sanarwar da tsagin jam’iyyar ya fitar a ranar Juma’a, shugabannin sun bayyana rawar da gwamnan ya taka a matsayin wacce ta saba da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Sanarwar dai na ɗauke ne da sa hannun Sanata Tony Adeniyi da Sanata Babafemi Ojudu.
Sanarwar dai ta yi zargin cewa kwanaki biyar kafin zaben gwamnan jihar Edo, gwamna Fayemi ya karɓi wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP a gidan gwamnatin jihar domin shirya abinda su ka kira da ‘juyin mulki’ ga APC.
Har wa yau, jam’iyyar ta zargi gwamnan da taka rawa wajen faɗuwar APC a zaɓen gwaman jihar Oyo na 2019.
To sai dai a ranar Laraba ɗaya tsagin jam’iyyar a jihar ta Ekiti ya sanar da korar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu da wasu ƙarin mutum 10 bisa zargin saɓawa umarninta.